Yaki da Cutar Sikari ko Diabetes a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 19.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Yaki da Cutar Sikari ko Diabetes a Najeriya

Sakamakon karuwar cutar Sikari a tsakanin al'umma a Najeriya, wata kungiya mai suna gidauniyar Safinatu ta tashi haikan wajen tallafawa masu dauke da cutar ta hanyar saya musu magani da abinci irin nasu kyauta.

Mafi aka sari dai an fi danganta cutar sikari ga dattijai to amma yanzu haka abin da ke cigaba da janyo hankulan alumma shi ne irin yadda cutar ke cigaba da shafar matasa kama daga mata zuwa maza. Wannan matsalar da ke haddasa tarin matsaloli ciki hadda kaiwa ga asarar rai ta sanya bullar gidauniyar da ke da mazaunita a Abuja tun a shekara ta 2010. Nasiru Yusuf Mani dake zama shugaban gidauniyar ya ce baya ga tallafi da suke bayarwa na magunguna, gidauniyar ta Safinatu na bada shawarwari ga masu wannan larura ta hanyar shirya musu bitoci da taruka.

Wannan kungiya inji shugaban nata na gudanar da aiyyukanta a jihohi da dama wanda suka hada da Nassarawa da Katsina da babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. Wannan aiki da suke yi dai ya sanya kungiyar tafiya har Amirka don nemo tallafi da nufin fadada irin taimakon da suke bawa jama'a. Wadanda suka amfana da wannan sun shaidawa DW cewa aikin kungiyar ya tallafa musu sosai wajen warware tarin matsalolin da wannan larura ta sanyasu a ciki.