Yaki da cin hanci a Nijar a shekarar 2014 | Siyasa | DW | 30.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da cin hanci a Nijar a shekarar 2014

Hukumar da gwamnatin Nijar ta kafa don baiwa 'yan kasar damar tona masu cin hanci a kasar ta fitar da rahotonta na shekara wanda wasu 'yan kasar ke cewa ba su gamsu da aikinta ba.

Sakamakon rahoton hukumar wadda ake yi lakabi da "tsanwar layi" ya nunar da cewa korafi 106 ne aka gabatar gabanta a cikin shekarar ta 2014. Daga cikin wannan adadi dai hukumar ta gudanar da bincike kan korafi 61 inda ta mika 9 ga bangaren shari'a na kasar don zurfafa bincike kafin su kai ga yanke hukunci kan irin matakin da za su dauka.

Shi dai wannan aiki da hukumar ta yi ya shafi ilahirin yankuna 8 da ke Jamhuriyar ta Nijar kamar yadda kakakin hukumar Alhaji Idi Abdu ya shaidawa sashin Hausa na DW. Daga cikin irin korafin da suka samu inji kakakin, hukumar tasu ta samu sukunin warwaresu da kanta don ko matsaloli ne da ke da nasaba da rashin fahimtar tsarin shari'a na Jamhuriyar ta Nijar.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012

Firaministan Nijar Malam Briji Rafini

To sai dai duk da wannan nasara da hukumar ta ce ta samu, a hannu guda ta koka kan rashin wadatar kayan aiki da ta ce na kawo mata cikas wajen gudanar da aiyyukanta kamar yadda suka dace inda ta kara da cewar duk da wannan wasu al'ummar kasar sun nuna gamsuwarsu dangane da yadda ta ke gudanar da aiyyukanta yayin da a hannu guda wasu ke korafin cewar ya zuwa yanzu ko da shari'a guda daga cikin jerin shari'un da aka fara kan abubuwan da aka bankado ba a kai ga kammalawa ba.

A cikin watan Agusta na shekara ta 2011 ne dai mahukuntan Nijar din suka kafa hukumar ta tsanwar layi don inda ake yinamfani da wata lambar waya don shaidawa jami'an hukumar dukannin watat badakala ta cin hanci da rashawa da 'yan kasa suka binciko domin ita hukumar ta bi diddiga a wani mataki na magance a wani mataki na neman kakkabe cin hanci da rashwa a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin