Yaki da cin hanci a Najeriya | Siyasa | DW | 23.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da cin hanci a Najeriya

A karon farko mukadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu ya jagoranci wani gagarumin gangami na wayar da kan jama’a a kan yaki da cin hanci da rashawa.

Kokari na wayar da kan ‘yan Najeriya na su ankara daga tunanen cewar yaki da cin hanci aiki ne na gwamnati ita ka dai da hukumomin da ta kafa shi ne muhimmin sako da mukadashin shugaban hukumar Ibrahim Magu ya isar ga ‘yan Najeriya. Ko wane tasiri suke ganin wannan ganagmin zai yi ganin yadda sauran hukumomin tsaro da masu wayar da kan jama'a da yaki da cin hanci suka shiga gangamin na zaburar da ‘yan Najeriya su kara bude idno su don fafutukar masu halin bera a kasar. Bullo da tsari na tonon silili a harkar yakar masu nuna halin bera da ke yin sama da fadi da dukiyar al'umma a Najeriyar ya kara zaburar da al'ummar kasar sanin irin rawar da ya kamata su taka a kan wannan aiki. Masu gangamin sun bi ta gaban majalisar dokokin Najeriyar wacce ke takun saka a kan kin amincewa da mukadashin shugaban hukumar a takadammar da ake ci gaba da sa idon ganin yadda za ta kaya.

Sauti da bidiyo akan labarin