Xi Jinping na jan zarensa a China | Labarai | DW | 05.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Xi Jinping na jan zarensa a China

 

Shugaban China Xi Jinping na ci gaba da jan zarensa a kasar duk da wasu 'yan matsaloli na tattalin arziki da kasar ke fusknata a baya-bayan nan, musamman rikicin cinikayyar da ke tsakininta da Amirka.

Shugaban na China wanda shi ne jagoran jam'iyyar gurguzu, ya jagoranci zaman shekara-shakara na mambobin jam'iyyar a wannan Talata.

Tun bayan hawansa karagar mulki shekara ta 2012, Shugaba Xi Jinping ya murkushe bangarori masu adawa da tsarin da kasar ke kai ta hanyar yaki da rasahawa da yake yi.

Batutuwan da suka shafi koma bayan tattalin arzikin ne dai za su mamaye zaman da suke yi a wannan Litinin.