Xi Jingping da Macron sun magantu kan yanayi | Labarai | DW | 06.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Xi Jingping da Macron sun magantu kan yanayi

Shugaba Xi Jinping na kasar China da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, sun ce babu batun sake matsayi dangane da yarjejeniyar sauyin yanayi da kasashe suka cimma a shekarar 2015.

Shugabannin manyan kasashen biyu da ke da hannu kan wannan yarjejeniya ta shekarar 2015, sun fadi hakan ne daidai lokacin da Amirka ta fara tsame kanta daga yarjejeniyar a hukumance.

Shugaba Macron wanda ke ziyarar aiki a China, ya ce batun ficewar Amurka daga yarjejeniyar zabi ne na kasar na ware kan nata da ta yi.

A ranar Litinin da ta gabata ne, Shugaba Donald Trump ya sanar da Majalisar Dinkin Duniya batun janyewar kasar daga yarjejeniyar.

Babu dai tabbas ko Mista  Macron ya gabatar da batun tsare wasu tsirarun kabilu na China a ganawar tasu da takwaran nasa, ganin yadda gabanin ziyararsa Chinar, masu rajin kare hakkin jama'a sun bukaci ya gabatar da batun ga Shugaba Xi Jinping.