WHO: Ba sauran Ebola a Laberiya | Labarai | DW | 09.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO: Ba sauran Ebola a Laberiya

Wannan bayani na Hukumar Lafiya ta Duniya na zuwa ne bayan kwashe kwanaki 42 ba a sami rahoton mai dauke da cutar ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana wanke kasar Laberiya a matsayin kasa da ba masu cutar Ebola a cikinta, bayan kwashe kwanaki 42 ba a sami rahoton mai dauke da cutar ba.

Sai dai an sami labarin wasu sabbin kamuwa da cutar a makotan kasar wato Saliyo da Guinea, kasashe biyu da suma wannan cuta ta yi muni a tarihin annobar a tsakanin kasashen yammacin Afirka.

Sai dai jami'ai da ma wadanda suka rayu bayan kamuwa da cutar sun bayyana cewa babu dalilin wani shagali kan rabuwa da cutar Ebola, kasancewar idan akwai mutum guda da ke kan iyaka da kasar mai dauke da wannan cutar na iya dalilin dawowarta.

Humukumar Lafiyar ta WHO ta tattara alkaluma da suka nunar da cewa fiye da mutane 4700 ne suka rasu ta sanadin wannan cuta a Laberiya , abin da ya sanya ta kasance kasa da tafi yawan wadanda suka rasu ta sanadin cutar tsakanin kasashen da suka kamu da ita.

Wannan cuta dai ta kashe sama da mutane 11,000 a yammacin Afrika.