Westerwelle ya gayyaci jakadan Amirka bisa zargin sauraron hirarrakin Merkel | Labarai | DW | 24.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Westerwelle ya gayyaci jakadan Amirka bisa zargin sauraron hirarrakin Merkel

Dukkan shugabannin jam'iyyun siyasa a Jamus sun fusata da wannan zargin na satar nadar tarhon shugabar gwamnati Angela Merkel.

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya gayyaci jakadan Amirka a Berlin John B. Ermerson don ya amsa tambayoyi bisa zargin cewar jami'an leken asirin Amirka sun yi satar nadar wayar tarhon Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel. Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin waje ta ce za a bayyana wa jakadan matsayin Jamus game da matakin wanda ta ce wani lamari ne na diplomasiya da ba a saba gani irinsa a tsakanin kawayen juna ba. Yanzu haka dai kungiyar lauyoyin Jamus ta fara gudanar da bincike a kan batun inda ta nemi hukumomin leken asirin Jamus da su yi mata bayani a kan abin da suka sani game da lamarin. Ita ma majalisar dokokin tarayya ta Bundestag za ta yi wani zama na musamman a kan batun. Shugaban kwamitin majalisar dokoki da ke sa ido kan ayyukan hukumomin leken asiri, Thomas Oppermann ya ce take-taken Amirka a yanzu ya tabbatar da fargabar da yake da ita game da aikace-aikacen hukumomin leken asirin Amirka na satar sauraron hirarrakin jama'a.

"Idan wannan zargin ya tabbata gaskiya, to hakan na zama wani mummunan cin amana. Saboda haka ya zama wajibi a gaggauta yin bincike domin fayyace gaskiya."

Dukkan shugabannin jam'iyyun siyasa a Jamus sun fusata da wannan batun na zargin satar nadar tarhon shugabar gwamnati. Thomas de Meziere shi ne ministan tsaron Jamus.

"Idan abin da muke ji yanzu ya tabbata, to wannan mummunan abu ne matuka. Amirkawa abokanmu za su kuma ci gaba da zama aminanmu, amma ba za mu yarda su wuce gona da iri ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahamane Hassane