Wata ′yar Chibok ta kubuta daga hannun Boko Haram | Siyasa | DW | 17.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wata 'yar Chibok ta kubuta daga hannun Boko Haram

Rahotanni daga Najeriya na cewar wata daliba da ke cikin 'yan matan da 'yan Boko Haram suka sace ta kubuta daga hannunsu har ma jami'an tsaro sun kaita Abuja.

Fadar shugaban Naajeriya ce dai ta bada labarin kubutar wannan daliba daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram wanda suka sace tare da wasu 'yan mata na makarantar Chibok kusan shekaru 3 da suka gabata. Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu babu karin bayani  game da suna da hali na lafiyar da take ciki a halin yanzu, tuni dai jami'an tsaron kasar suka dauki yarinyar zuwa Abuja kamar dai yadda kakakin Shugaba Buhari Femi Adesina a shaidawa wakilinmu na Abuja Ubale Musa.

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro ba su yi karin haske game da wannan lamari ba kuma manema labarai ba su kai ga yi tozali da ita wannan yarinya ba don jin yadda aka yi ta kubuta daga hannun mayakan kungiyar ta Boko Haram. A ranar Asabar ta mako jiya ne dai aka kai ga sanarwar gano karin wasu yan matan 82 bayan wata musayar da ke zaman irinta ta farko ga bangarorin guda biyu. To sai dai kuma duk da alamun sauyi daga dukkan alamu bangarorin na kallon juna da idanu na tsanaki sakamakon karuwar ta'azarar hare-hare. 

Sauti da bidiyo akan labarin