Wata cuta ta halaka mutane 80 a Bauchi | Labarai | DW | 28.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata cuta ta halaka mutane 80 a Bauchi

An dai shiga bincike don gano dalilai da suka sanya wannan cuta da ke da alaka da zazzabi ke halaka mutane a kauyen na Tiyi a Bauchi Najeriya.

Wani zazzabi mai zafi ya yi sanadi na rayukan mutane 84 a wani kauye na Tiyi a karamar hukumar Warji jihar Bauchi Arewa maso Gabashin Najeriya. Wakilin DW a Bauchi Aliyu Muhammad Waziri da ya ziyarci wannan kauye ya ce tuni likitoci suka shiga aikin bincike kan gano wane irin zazzabi ne haka mai zafi da ke halaka mutane, kamar yadda ya halaka 'ya'yan wannan mata:

"Zazzabi ne hadi da maleriya sai dai ya yi zafi sosai ya halaka yarana biyu."

Manya da yara ne dai ke hakala kan wannan cuta da su kansu al'umma na kauyen ke cewa ba su san wace iri ba ce.