SiyasaJamus
Wasu dalilan tabarbarewar ilimi a Najeriya
July 1, 2021Talla
Masana da masu fashin baki kan harkokin ilimi na ci gaba da bayyana irin yadda ilimi ke kara tabarbarewa musamman ma a arewacin kasar.
Dalilai da dama ne dai suka sanya daliban rashin katabus a banan, wadanda suka hada da rufe makarantu da aka yi saboda gudun yaduwar cutar COVID-19. Haka ma akwai wadanda ke ganin maida hankali da matasa ke yi a shafukan sada zumunta na zamani maimakon karatu yadda ya dace. Faduwar dai ta yi munin da ba a taba ganin irinta ba a kasar.