Wasannin Bundesliga na karshen mako | Zamantakewa | DW | 06.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wasannin Bundesliga na karshen mako

Kamar yadda aka saba kungiyoyin kwallon kafa daban daban na Jamus sun fafata a karshen mako a cigaba da wasnnin kakar Bundesliga ta bana

A wasanin kwallon kafa na Bundesliga na Jamus da aka yi a karshen mako, kungiyar kwallon kafa ta Hertha Berlin ta doke Stuttgart 3 da 1, kana Wolfsburg ta samu galaba kan Nürnberg 2 da nema.

Mainz ta tashi 3 da 3 da kungiyar Leipzig. Bayern Munich ta doke Hannover 3 da 1, ita kuma Werder Bremen da Borussia Dortmund sun tashi 2 da 2. Sannan kungiyoyin Mönchengladbach da Hoffenheim sun tashi 2 da 2.