1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Gasar shiga Olympics na 2020

Mouhamadou Awal Balarabe
February 10, 2020

Tawagar kwallon kwando ta mata ta Najeriya ta cancanci shiga gasar Olympics a daidai lokacin da wani dan asalin kasar da ya girma a Girka ke tashe a fagen NBA na Amirka

https://p.dw.com/p/3XZQr

Babbar kungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya D Tigress ta samu tikitin shiga wasannin Olympics na 2020 a Tokyo, duk da cewa ta sha duka 64-70 a hannun Sabiya a ranar Asabar, a wasan rukuni na biyu a gasar wasannin neman cancanta. Tawagar Najeriya ta samu wannan dama ce bayan kokarin Mozambik na cancanta ya ci tura sakamakon mummunan duka ci 49-124 a hannun Amerika da ke rike da kofin duniya na basket-ball.

A ranar Lahadi ma 'yan matan na Najeriya sun kara da takwarorinsu na Amerika wasan rukuninsu na uku, wanda hakan ba zai yi tasiri ba a wasannin neman shiga wasannin Olympics na 2020.

Hukumar kwallon Kwando ta Najeriya NBBF ta kafa tarihi wajen kasancewa kungiya daya tilo da za ta samu wakilai biyu a Gasar Olympics.