IOC ita ce kungiyar da ke shiryawa da kuma kula da wasannin tsalle-tsalle da na motsa jiki na Olympics da aka saba yi duk shekara hudu lokacin hunturu da kuma bazara.
A cikin shekarar 1894 ce Baron Pierre de Coubertin ya kafa hukumar ta Olympics ta duniya kuma tun wannan lokacin ne hukumar ke shirya wasanni tsakanin kasashen duniya har ma daga bisani ta ware wasannin Olympics na matasa zalla da ake yi sau daya a kowadanne shekaru hudu.