Najeriya: Me za a yi ga masu bai wa IS kudi?
June 24, 2026
Wannan dai wani muhimmin mataki ne, na bankado wadannan kamfanonin na Najeriyar da wani mutum guda. Tuni ta dauki mataki, na sanya musu takunkumin gudanar da duk wasu harkokin kudi. Samun kamfanonin Najeriya har uku a cikin wannan harka ta daukan nauyin samar da kudi ga kungiyar 'yan ta'ada ta ISIS, ya zo a daidai lokacin da kasar ke neman hanyoyin da za ta dakile kafofin da kungiyoyin ke samun kudi a yakin da sojoji ke yaki da kungiyoyi kamar ISIS da kawayensu.
Daga wanne kasashe ake taimakon IS?
Kamfanonin na Najeriya na cikin mutane uku da kamfanoni shida da suke a kasashen Siriya da Turkiya da Faransa da Najeriya, kamar yadda kakakin ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Amurka Thomas Pigott ya shaidar cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta nunar da cewa kamfanonin uku na Najeriyar, biyu a Lagos suke yayin da daya kuma yake a birnin Kano da ke arewacin kasar. Kamfanonin na amfani da kudin Crypto, wajen aika kudin ta hanun masu sana'ar canjin kudi. Akwai kuma masu samar da bayanai, na yadda masu kai hare-haren ke harhada abubuwa masu fashewa da suke amfani da su.
Najeriya na kawance kan tsaro
Katse hanzari ne dai, na samar da kudi ga kungiyar da ke kai da komowa a tsakanin kasashen duniya. Ana kallon wannan a matsayin tasirin kawance da Najeriya ke da shi da kasar Amurka, inda Washington ta yi alkawarin bai wa Abuja taimako a fanin tsaro da ake sa ido da fatan ganin tasirinsa.
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar