Najeriya: Amurka za ta magance rashin tsaro?
February 11, 2026
Da sunan yaki da ta'adda dai Amurkan ta ce karin sojoji 200 ne ke shirin isa Tarayyar Najeriyar, ko bayan bude wani sabon sansanin jiragen ya ki marasa matuka a jihar Borno. Sannu a hankali dai Najeriyar na shirin zama sabon sansanin Amurkawan a yankin Sahel, duk da cewar dai tun shekaru kusan 20 ne Amurkan ke kamun kafa a kokarin kafa sansanin sojan. Ga dukkan alamu, a yanzu ne babban burin nata ke shirin ya tabbata. Tun daga zargin kokarin kare Kiristoci dai, masu mulkin Najeriya suka mika wuya ga bukatun na Amurka.
Duk da cewar dai an kira batun tsaro da kare ta'addanci dai, tuni karin tasirin na Amurka cikin batun tsaron ke daukar hankali cikin kasar da a baya take fadin tana da 'yancin yin na gaban kai. Tun daga jamhuriya ta farkon fari Najeriyar ta sa kafa ta shure bukatar sansanin sojan Birtaniya, kafin kuma daga baya Abujar ta ce a kai ga kasuwa cikin batun shigar Amurka. Sashen arewacin Najeriyar dai, na zaman tungar rikicin na ta'adda. Kama daga sansani zuwa jibge sojan dai, a sashen na Arewa ne ake shirin ganin rawa da kila ma tasirin na Amurka.
Duk da cewar dai Amurkan na zaman ta kan gaba cikin batu na makamai da kila ma na kwarewa, shigar kasar zuwa Afghanistan da Iraki da ma a Siriya ta kare ba tare da sauya da dama cikin batun na tsaro ba. Kyaftin Abdullahi Bakoji dai tsohon jami'in soja ne a Tarayyar Najeriyar, kuma ya ce da babban hatsari ga dogaro da kasashen na waje bisa tsaro da kila ma na makoma. Daukacin karatun Amurkawan har ya zuwa yanzu, yana fitowa ne daga jami'an na Washington a maimakon na Abujar da ke karatun kurma.
Kuma wani yunkurin 'yan majalisar dattawa na sanin abun da ke akwai cikin batun na hada kai, ya kare da Abujar sa kafa ta shure bukatar. Abun kuma da yake kara jawo damuwa, cikin kasar da ke kara shiga duhu a batun rashin tsaron a halin yanzu. Ko bayan batu na karfin soja, tuni dai kawancen na Amurka ya fara nuna alamun tasiri tare da wasu 'yan majalisar wakilan na Amurka biyar mika bukatar wata dokar da za ta haramtawa masu adawa kamar tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso shiga kasar ta Amurka.