1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Wani na son tayar da abin fashewa a ofishin jakadancin Iran

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 19, 2024

Jami'an tsaron sun yi wa harabar ofishin jakadancin kawanya yanzu haka

https://p.dw.com/p/4ezA0
Hoto: Benoit Tessier/REUTERS

'Yan sandan Faransa sun killace ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris, bayan da wani mutum ya yi ikirarin tayar da wani abin fashewa da ke jikinsa a ciki.

Karin bayani:Iran ta ce babu wani abin fargaba kan fashewar bam a Isfahan

Gidan Rediyon Faransa Europe 1, ya wallafa a shafinsa na X cewa jami'an tsaron sun yi wa harabar ofishin jakadancin kawanya yanzu haka, sannan sun umarci jama'a su kaucewa wurin baki-daya.

karin bayani:Amurka za ta kakaba wa Iran takunkumi saboda harin Isra'ila