1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shugabanci a Venezuela

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 4, 2019

Shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya sanya kafa ya yi fatali da wa'adin sake gudanar da zaben shugaban kasa, da wasu kasashe kungiyar EU suka dibar masa.

https://p.dw.com/p/3CfYB
Venezuela Krise | Präsident Nicolas Maduro in Caracas
Shugaban kasar Venezuela Nicolas MaduroHoto: Reuters/Miraflores Palace

Da dama dai daga kasashen kungiyar ta Tarayyar Turai EU, sun bayyana cewa za su amince da jagoran adawa  Juan Guaidó wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban riko a Venezuelan. Sai dai hakan bai sanya Maduro ya yi ko dar ba, inda yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin ya nunar da cewa ba ya shakka ko kuma tsoron duk wani matsin lamba da kasashen ketaren ke yi masa. Jamus da wasu kasashe da dama na kungiyar ta EU dai, sun bai wa Maduro kwanaki takwas domin ya shirya gudanar da sabon zaben shugaban kasa, ko kuma su amince da jagoran adawar. Tuni ma dai kasar Spain ta bi sahun Amirka da wasu kasashen Latin Amirka wajen amincewa da Guaidó a matsayin shugaban kasar Venezuelan na riko.