1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ana boren adawa da mamayar Rasha a Ukraine

March 6, 2022

Mutane sama da 3,500 ne hukumomin Moscow suka kama da laifin fitowa zanga-zanga duk da gargadin da aka yi musu a ranar Asabar cewa duk wanda ya fito za a hukunta shi. 

https://p.dw.com/p/485nZ
Proteste in Moskau
Hoto: Sergei Fadeichev/TASS/dpa/picture alliance

Jami'an tsaro a birane 21 na kasar Rasha sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da mamayar da Shugaba Vladimir Putin ke yi wa kasar Ukraine.

Hakan na zuwa ne yayin da a Ukraine, Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya zargi dakarun Rasha da yunkurin kai farmaki a birnin Odessa da ke kusa da teku. Zelenskyy ya ce yin hakan mummunan laifi ne a harkar yaki.

Shugabannin Ukraine sun ce a wannan Lahadi, Rasha ta ci gaba da kai hare-hare da jiragen sama a birnin Mykolaiv, inda sojojin Rasha da na Ukraine suka yi musayar wuta.