1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Taimakon Amurka na tafe

Abdullahi Tanko Bala
May 14, 2024

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyarar ba zata domin tabbatar wa Ukraine cewa Amurka na bayanta kuma za ta aika mata karin taimakon makamai a yakin da ta yi da Rasha

https://p.dw.com/p/4fqZ9
Ukraine | Antony Blinken da Volodymyr Zelensky
Ukraine | Antony Blinken da Volodymyr ZelenskyHoto: Ukrainian Presidential Press Office/AP/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya shaida wa Ukraine cewa taimakon makaman Amurka na kan hanya domin tunkarar kalubalen Rasha.

Babban jami'in diflomasiyar na Amurka wanda ya kai ziyarar ba zata zuwa Kiev ya shaida wa shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky cewa Amurka na sane da mawuyacin halin da ake ciki amma tallafin makamanta na tafe kuma za su kawo sauyi a yakin da ta ke fafatawa da Rasha.

Sai dai kuma a ci gaba da farmakin da ta ke yi a arewa maso gabashin Ukraine, Rasha ta kame wurare da dama ciki har da wasu kauyuka bakwai a cewar manazarta.