1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinci

Ukraine ta zargi Rasha da neman haddasa yunwa

Binta Aliyu Zurmi SB
June 11, 2022

Zelensky ya ce matsalar abainci da za a fuskanta sai ya nunka wanda aka gani a yanzu, idan Rasha ta ci gaba da hana fitar da hatsi sakamakon yakin da ke faruwa.

https://p.dw.com/p/4CZe5
Singapur | Videoansprache von Wolodymyr Selenskyj am Shangri-La Dialog
Hoto: ROSLAN RAHMAN/AFP

Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya yi gargadin samun duniya na gab da shiga matsalar yunwa a saboda hana fitar da hatsi da ke jibge a tashoshin ruwan kasar da Rasha ke ci gaba da yi.

Da yake jawabi ga taron sulhu da ya gudana a Singapore ta kafar bidiyo, Zelensky ya ce abin da duniya ke fuskanta yanzu haka duk wasan yara ne, muddin aka ci gaba da tafiya a haka duniya za ta shiga wani hali na matsananciyar yunwa a kasashe da dama a nahiyar Afirka da Asiya da ba a ga irin ta ba.

Kazalika ya ce matsalar ta yunwa ka iya janyo rikice-rikicen siyasa da ka iya kai wa ga kifar da gwamnatoci.

Mahukuntan na Kiev na zargin Moscow da sace hatsin da suka hana a fitar da shi, a yayin da farashinn kayayyakin masarufi ke tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya, Moscow na dora alhakin hakan an kan makwabciyarta Ukraine.