Ukraine ta yi fatali da tallafin Rasha | Labarai | DW | 22.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine ta yi fatali da tallafin Rasha

An kai 'yan kwanaki da dama yanzu motoci makare da kayyayakin tallafin da gwamnatin Rasha ta turawa al'ummomin da ke bukata a yankin gabashin Ukraine suna zaune a bakin iyaka.

Mai magana da yawun majalisar tsaro na Ukriane Andrey Lisenko, ya ce manyan motoci 90 ne Rasha ta turo ba tare da amincewar gwamnatin Ukraine ba, kuma wadannan motoci ba su sami rakiyar kungiyar agaji ta Red Cross ba, wanda tanadi ne na dokar kasa da kasa idan har za a bada irin wannan tallafi.

Shugaban hukumar leken asirin kasar ta SBU, Valentin Naly-Viat-Schenko ya zargi Rasha da mamaya bayan da wasu daga cikin manyan motocin suka shiga kasar ta yankin Donestk.

Ma'aikatar harkokin wajen Moskow kuwa a nata waje, ta bayyana cewa duk wani zance na tsaikon da aka samu wajen kai kayyakin agaji ta riga ta kammala shi. Bisa bayyanan da mahukuntan Rashar suka bayar dai, motocin na dauke da kayyakin da suka hada ruwan sha da abincin yara da sauran ababen da dan adam ke bukata na yau da kullun.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu