Ukraine ta sa wa wasu ′yan Rasha takunkumi | Labarai | DW | 08.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine ta sa wa wasu 'yan Rasha takunkumi

Mahukuntan Ukraine sun sanar da sanya takunkumi kan wasu 'yan asalin kasar Rasha da kuma wasu kamfanonin Rashan da ke yin kasuwanci a Ukraine din.

Firaministan Ukraine dinArseniy Yatsenyuk ya ce sun dau wannan aniya ce domin mutanen da yawansu ya kai 172 da kamfanonin na Rasha na taimakawa 'yan aware da ke rikici da dakarun gwamnatin Ukraine din a gabashin kasar.

To sai dai Mr. Yatsenyuk ya ce kafin wannan tankunkumi ya fara aiki sai majalisar dokokin Ukraine din ta tafka muhawara ta amincewa da shirin.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Rasha ta haramta shigar mata da kayayyaki musamman ma na abinci daga wasu kasashen Turai a wani abu da ake kallo a matsayin martani kan takunkumin da kasashen na Turai da Amirka suka kakaba wa Moscow.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal