1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta dau tsattsauran mataki kan Rasha

Zulaiha Abubakar
November 30, 2018

Rahotanni daga Kiev babban birnin kasar Ukraine sun baiyana yadda gwamnatin kasar ta haramta wa al'ummar Rasha wadanda shekarun su suka fara daga 16 zuwa 60 shiga kasar.

https://p.dw.com/p/39D6p
Hoptivka-Kontrollpunkt an der Grenze zwischen Ukraine und Russland
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Tuni dai gwamnatin Rasha ta yi Allah wadai da wannan kudiri na Ukraine ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar, Maria Zakharova tare da jaddada gargadi ga Ukraine kan ta kiyayi daukar zugar kasashe irin su Amirka.

  Ukraine dai ta dauki wannan mataki ne sakamakon kame jiragen ruwanta har guda uku da Rasha ta yi a makon daya bagata.