Ukraine da ′yan tawaye sun cimma tsagaita wuta | Labarai | DW | 05.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine da 'yan tawaye sun cimma tsagaita wuta

Kungiyar OSCE ta tabbatar da sanya hannu kan shirin tsagaita wuta a gabashin Ukraine tsakanin gwamnatin Kiev da 'yan aware.

Kungiyar tsaro da hadin kai a Turai, OSCE ta ce wakilan gwamnatin Kiev da na 'yan tawaye magoya bayan Rasha sun amince sun ayyana tsagaita wuta a wannan Jumm'a. Heidi Tagliavini da ke zama wakiliyar kungiyar ta OSCE a gun taron tattauna batun rikicin Ukraine a Minsk babban birnin kasar Belarussia ta ce wakilan bangarorin da ke rikici da juna sun sanya hannu kan wata takarda da ta ayyana fara tsagaita wuta da karfe 3 agogon GMT a wannan Jumma'a. Sai dai duk da shirin tsagaita wutar an jiyo jagoran 'yan tawaye da ke rike da yankin Luhansk na cewa 'yan tawaye masu ra'ayin Rasha za su ci gaba da hankoron ballewa daga Ukraine.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman