1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na ikirarin nasara a Sievierodonetsk

Abdul-raheem Hassan
June 4, 2022

A cigaba da yakin da ke daukar hankali a gabashin nahiyar Turai, kasashen Ukraine da Rasha na ikirarin nasara a birnin Sievierodonetsk da ke gabashin Ukraine.

https://p.dw.com/p/4CI96
Ukraine - Zerstörung in Luhansk
Hoto: Serhii Nuzhnenko/REUTERS

Dakarun Ukraine sun ce sun kwace iko da wani yankin Sievierodonetsk a wani farmakin da ba kasafai ake kaiwa dakarun Rasha hari ba, a dai-dai lokacin da sojojin Moscow ke cigaba da dannawa cikin yankin.

Babu tabbaci kan ikirarin kwace yankin da Ukraine ke yi, yayin da ita ma Rasha ta ce dakarunta na samun nasarori a yankin. Sai dai wannan shi ne karo farko da gwamnatin Kyiv ta yi ikirarin kaddamar da wani babban hari a Sieverodonetsk bayan kwanaki na barin wuta.

A ranar Juma'a 3 ga watan Yunin 2022 aka cika kwanaki 100 da fara yaki tsakanin Ukraine da Rasha, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da tilasta miliyoyi jama'a hijira da rikita tattalin arzikin duniya.