Ukraine da Rasha al′umma daya ce inji Putin | Labarai | DW | 18.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ukraine da Rasha al'umma daya ce inji Putin

A jawabin da ya yi a taron cika shekar guda da hadewar Kirimiya da Rasha, shugaban na Rasha ya ce tushen al'ummomin daya ne.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada wa wani taron gangamin bikin cika shekara daya da hadewar yankin Kirimiya da Rasha cewa Ukraine da Rasha al'umma daya ce. A jawabin da ya yi a dandalin Red Square Putin ya ce Kirimiya da Rasha ba sun hade ne saboda wata manufa ta fadada yanki ko wasu dubarun yaki ba, amma ya ce yankin tsibirin tushensu ne na ruhi da kuma kasa. Ukraine da kasashen yamma sun sanya wa Rasha takunkumai a kan abin da suka kira mamaye yankin tsibirin da ke tekun Bahar Aswad da Rasha ta yi ba bisa ka'ida ba, sannan ta ci gaba da goyon bayan boren da 'yan awaren gabashin Ukraine ke yi, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane 6000 tun farawansa a cikin watan Afrilun bara.