1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunta wasu mutane masu hannu a shan gubar Alexeï Navalny

Abdoulaye Mamane Amadou
October 14, 2020

Kungiyar Tarayar Turai na shirin daukar matakan ladabtarwa kan wasu mutane shida a Rasha da ta zarga da hannun wajen shayar da madugun adawar Rasha Alexeï Navalny guba.

https://p.dw.com/p/3jvhK
Alexej Nawalny
Hoto: YouTube - vDud/Reuters

Wata majiya daga hukumar EU tace an aike wa kasashe membobin kungiyar bukatar daukar muhimman takunkuman a rubuce domin su tabbatar da amincewarsu, kafin wallafa sunayen wadanda lamarin ya shafa da kuma soma aiki da matakin a gobe Alhamis.

Tun daga farko dai ministocin harkokin wajen kasashen da suka gana a ranar Litinin din da tagabata sun yi na'am da gagarumin rinjaye kan shawarwarin takunkuman da kasashen Jamus da Faransa suka gabatar, kana kuma babban jami'in diflomasiyar Turai Josep Borrell ya bayyana cewa daukacin kasashen sun aminta da matakan.