1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Turkiyya na bincike kan musabbabin gobarar gidan gala

April 2, 2024

Adadin mutanen da suka mutu na ci gaba da karuwa a yayin gyaran wani gidan gala a kasar Turkiyya. Hukumomi kasar sun tsare mutum shida da ake zarginsu da hannu wajen tada gobarar a birnin Istanbul.

https://p.dw.com/p/4eMoB
Gidan wasan da aka samu tashin gobara a Istanbul
Gidan wasan da aka samu tashin gobara a IstanbulHoto: ISTANBUL FIRE DEPT./EPA

Kimanin mutane 29 ne suka mutu sakamakon gobarar gidan galan a birnin Istanbul yayinda wasu da dama suka jikkata. Jami'an hukumar kashe gobara sun bayyana cewa gobarar ta tashi da misalin karfe 12:47 na dare agogon Turkiyya wato 9:47 agogon UTC, a wani rukunin gidajen da ke yankin Turai na kasar.

Karin bayani: An kai hari wata mujami'a a Turkiyya 

An rufe gidan galan gabanin azumin watan Ramadan domin gudanar da wasu gyare-gyare kafin daga bisani gobara ta tashi a wajen, kamar yadda jaridar Hurriyet  ta rawaito.

Karin bayani:  Turkiyya: Imamoglu ya lashe zaben Magajin Garin Santanbul

Magajin garin birnin da aka sake zabarsa a kwana-kwanannan Ekrem Imamoglu ya isa wajen da lamarun ya faru, tare da fatan cewa ba a samu karin wadanda suka rasa rayukansu ba.