1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari wata mujami'a a Turkiyya

January 28, 2024

Wasu mahara sun kai hari wata mujami'ar Italiya da ke birnin Santabul na kasar Turkiyya, inda mutum daya ya rasa ransa.

https://p.dw.com/p/4blZO
Hoto: Ozan Kose/AFP

Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya ya ce wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kaddamar da hari a wata mujami'ar Italiya da ke birnin Istanbul, inda mutum daya ya rasa ransa.

A cikin sanarwar da ministan ya fitar, ya ce maharan sanye da takunkumin rufe fuska sun kai harin ne da safiyar wannan Lahadi a Mujami'ar Santa Maria a lokacin da ake tsaka da gabatar da ibada.

A yayin da ya ke Allah wadai da harin, Yerlikaya ya ce, an fara gudanar da bincike kan hari kana mahukunta na aiki domin kama maharan. Kawo yanzu dai ba a san manufar kai harin ba.

A watan Disambar 2023 hukumomin tsaron Turkiyya suka kama mutum 32 da ake zargi suna da alaka da kungiyar IS da suke shirya kai hare-hare kan mujami'u da kuma offishin jakadancin Iraqi.