Turkiya ta koma yaki da kungiyar ′yan awaren PKK | Siyasa | DW | 01.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turkiya ta koma yaki da kungiyar 'yan awaren PKK

Matakin gwamnatin Turkiya na koma wa ga yakar kungiyar 'yan awaren Kurdawa ta PKK ya kawo karshen shirin zaman lafiyarsu dama barazana ga dangantakar kasar da yankin 'yancin cin gashin kan Kurdawa na arewacin Irakin.

An kara shiga cikin rashin tabbas biyo bayan sauyin alkiblar gwamnatin Turkiya a kan manufarta da ta shafi Kurdawa. Shin wane irin martani Kurdawan za su mayar ganin cewa shugaban Turkiya Tayyip Erdogan ya dakatar da shirin zaman lafiya. Shin wane abokin dasawa ko kuma abokin gabar kasashen yamma a tsakanin Kurdawa mazauna kasashen Siriya da Iraki?

Matsayin Massoud Barzani kan wannan rikici

Birinin Erbil shi ne mazaunin shugaban yankin cin gashin kan Kurdawa da ke arewacin Iraki. A makon da ya gabata shugaban gwamnatin yankin Massoud Barzani ya yi wa kamfanin dillancin labarun AFP bayani game da dangantakarsa da kungiyar 'yan awaren Kurdawa ta PKK da kuma shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan.

"Idan Turkiya ta ba da shawarar samun maslaha cikin lumana amma PKK ta yi watsi da ita, to a shirye muke mu dauki duk wani mataki kan PKK. To amma idan Turkiyya na son ta fake da matsalar da ke tsakaninta da PKK domin ta yake mu, to a shirye muke mu kare kanmu."

An dade ana zaman dar-dar a dangantaka tsakanin yankin 'yancin cin gashin kan Kurdawa a arewacin Iraki da kungiyar PKK. Dalilan da suka sa Massoud Barzani kin lamirin PKK na da nasaba da tarihinsu na baya-bayan nan. Bayan yakin Golf a shekarar 1991 lokacin da MDD ta sanya takunkumi kan Irak karkashin shugaba Saddam Hussein, Kurdawan arewacin Irakin ba su samu wani taimako daga 'yan uwansu ba, domin PKK ta bari an toshe hanya daya tilo da ta hade Turkiya da yankin Kurdawa a arewacin Iraki, abin da har yanzu yake zukatan mazauna wannan yanki mai 'yancin cin gashin kai.

Bayan kutsen da Amirka ta jagoranta da ya kai ga hambarar da Saddam Hussein a shekarar 2003, an sake maimaita wannan lamarin. Sojojin sa kai na kungiyar PKK da suka mamaye tsaunukan Kandil da ke can kuryar yankin Kurdawan arewacin Iraki, suna kuma kai farmaki kan Turkiyya daga yankin, sun ci karo da turjiya daga Barzani. A wannan yanki ne kuwa a 'yan kwanakin nan jiragen saman yakin Turkiyya suka kai farmaki kan sansanonin da ake zargi na 'yan tawayen PKK ne.

Shawarar Massoud Barzani ga PKK

Kalaman da shugaban yankin cin gashin kan Kurdawa na arewacin Iraki Massoud Barzani ya yi game da halin da ake ciki ya nuna fili irin dadaddiyar gabar da ke tsakaninsa da kungiyar PKK.

 "Kwanaki kalilan da suka wuce Erdogan ya bukaci PKK ta ajiye makamanta sannan ta koma zauren majalisar dokoki don warware matsalolinta. A gani na wannan shawara ce mai kyau."

Da taimakon Amirka ne dai a bara aka taka wa mayakan kungiyar IS biriki lokacin da suke dab da shiga yankin Erbil bayan sun kwace birnin Mossul, abin da shi kan shi Barzani ya ce in ba don Amirka ba da ba a shawo kan lamarin ba. Hakazalika da taimakon kasashen yamma ciki har da Jamus hadaddiyar kungiyar Kurdawa ta Pershmerga suka tinkari IS.

Barazanar da Kurdawan arewacin Siriya suka fuskanta daga IS ta zama hujjar da Amirka ta shiga yakin basasan Siriya. Da kuma taimakonn jiragen saman yakin Amirka da Kurdawan Pershmerga na Iraki aka karya lagon kofar rago da IS ta yi wa yankin iyaka da Kobane cikin watan Satumban bara. Rundunar sojan kare Kurdawa da a shekarar 2012 a hukumance aka dora mata nauyin mai kare al'umar Kurdawa a yankin kan iyakar Siriya da Turkiyya, har yau ita ce ke tinkarar IS.

Muhammad Nasiru Awal