Turkiya ta kama sama da mutane 1000 a yakin da take da ′yan tarzoma | Labarai | DW | 27.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta kama sama da mutane 1000 a yakin da take da 'yan tarzoma

A kokarinta na yaki da mayakan IS da PKK ya zuwa yanzu Turkiya ta kama mutane da dama ciki kuwa har da 'yan kasashen waje.

Türkei Recep Tayyip Erdogan PK zu Angriffen auf Syrien

Recep Tayyip Erdogan

Turkiya ta tsare wasu mutane 1,050 cikin aiyukan da take yi wajen ganin ta fatattaki mayakan sakai daga kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama dama kungiyar mayakan sakai daga Kurdawan PKK .

A cewar Firaminista Ahmet Davutoglu na Turkiya a kamen da suka yi a ranar Litinin din nan cikin wadanda aka cafke cikin mayakan masu tada kayar baya akwai 'yan kasashen waje hamsin zuwa sittin.

Firaminista Ahmet Davutoglu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na ATV na kasar Turkiya.