Turkiya: An kama wasu lauyoyi | Labarai | DW | 16.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya: An kama wasu lauyoyi

Kungiyar lauyoyi a Turkiya ta sanar da cewa jami'an 'yan sanda sun tsare wasu lauyoyi guda takwas a ci gaba da kokarin murkushe magoya bayan Kurdawa 'yan fafutuka a kasar.

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan

Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyan ya sanar da cewa zai fadada ma'anar ta'addanci a kasar, inda zai hadar da malaman makarantu da jami'oi da kuma 'yan jarida da ma 'yan adawar kasar. Tsare wadannan lauyoyi dai ya biyo bayan cafke wasu malaman makaranta guda uku a Turkiya bisa zarginsu da farfagandar ayyukan ta'addanci da aka yi a jiya Talata. Su dai malaman an kama su ne bayan da suka sanya hannu kan wani koke da ke yin tir da matakan da sojojin kasar ke dauka a kan jam'iyyar Kurdawa ta PKK a kasar.