Turai na tattauna batun bakin haure | Siyasa | DW | 20.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turai na tattauna batun bakin haure

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun shiga rana ta biyu a taron kolin da suke yi a birnin Salzburg na kasar Austriya in da suke tattaunawa kan batun ficewar Birtaniya daga kungiyar da tsaro da kuma batun bakin haure

 A ranar Laraba Firaministan Birtaniya Theresa May ta yi kira ga Kungiyar ta EU da ta nuna sassauci kan matsayinta a tattaunawar kan batun ficewar da ake wa lakabi da Brexit. Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani a cikin wannan rahoto da ya hada mana.

Taron kolin na wannan Alhamis na zuwa ne kwana guda bayan da Firaministan Birtaniya Theresa May ta yi kira ga takwarorinta na Kungyiar Tarayyar Turai EU da su bi sahunta su kuma yarda da matsayin Birtaniya a tattaunawa kan ficewar kasar daga EU da ake wa lakabi da Brexit domin cimma abin da ta kira yarjejeniya mai kyau musamman dangane da makomar dangantaku tsakanin bangarorin biyu.

"Idan muna son mu cimma nasara a karshe, kamar yadda Birtaniya ta nuna matsayinta, to ya zama wajibi ita kuma EU ta fito karara ta nuna matsayinta. Ina da kwarin gwiwa idan muka jajiirce muka yi kyakkyawan fata za mu kai ga cimma wata yarjejeniya kyakkyawa da za ta dace dukkan bangarorin guda biyu."

Ita dai Firaministan ta kare shawarar da kasarta ta bayar kan batun kwasta da yarjejeniyar kasuwanci da EU tana mai cewa za ta ba da damar yin kasuwanci ba da wata matsala ba da za ta kuma warware wani rikici na kan iyaka da ka iya kunno kai tsakanin lardin Ireland ta Arewa da ke karkashin Birtaniya da Jamhuriyarn Ireland wada memba ce a Kungiyar EU.

A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira da a mutunta juna a tattaunawar tsakanin Birtaniya da Kungiyar EU da dukkansu biyu ke neman karfafa dangantaka bayan Brexit.

 "Ina fata ficewar Birtaniya wato Brexit za ta gudana cikin kyakkyawan yanayi tare da mutunta juna, kana akwai yiwuwar karfafa hadin kai a wasu bangarorin wato kamar tsaron cikin gida da ma a ketare."

Taron kolin na kuma tattaunawa kan batun bakin haure da har yanzu ke ci gaba da kawo rarrabuwar kai tsakanin membobinta a cewar Federica Moghereni babbar jami'ar kula da harkokin ketare a EU wadda ita ma ke halartar taron

.

"Zan jawo hankali game da ayyukan da muke yi a kan manufofin da suka shafi bakin haure, musamman na hulda mai karfi da muka kulla Kungiyar Tarayyar Afirka. A ranar Lahadi mai zuwa akwai wata ganawa ta manyan jami'ai a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Antonio Guterres da Moussa Faki shugaban hukumar tarayyar Afirka za su halarta don bitar aikin da muke yi da zan iya cewa ana samun sakamako mai kyau na zuba jari da neman kasashen duniya su kara yawan kudin da suke sakawa a hadin gwiwar da muke yi da Afirka."

An ruwaito cewa taron kolin na birnin Salzburg a wannan Alhamis ya amince da shirya wani taron koli na musamman da zai gudana a birnin Brussles a ranaikun 17 da 18 ga watan Nuwamba a wani mataki na kammala yarjejeniyar.

Sauti da bidiyo akan labarin