Turai: Mafaka ga mata da aka yi wa kaciya | Siyasa | DW | 09.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turai: Mafaka ga mata da aka yi wa kaciya

Duk da wannan mataki da EU ta dauka, yara matan da aka haifa a Turan ma ba su tsira daga wannan al'ada ba, domin kuwa a nan din ma suna fadawa cikin hadarin yi musu kaciyar.

Wadanda ke wannan al'ada ta yi wa yara mata kaciya dai na amfani ne da almakashi ko kuma wuka wajen yanke matucin yara mata. Su kan yi musu kaciyar ne ba tare da sun kashe wajen domin rage musu radadi da zafi ba, kana sau tari ba ma sa tsabtace wukar ko almakashi da suke amfani da su wajen yin kaciyar, wanda hakan ke da matukar hadari wajen yi wuwar kamuwa da cututtuka. Bayan sun kammala su kan dinke gurin inda a wasu lokutan su kan hada da mafitsara wanda ke janyo ciwon jiki da kuma damuwa na har abada ga wadannan 'yan mata da aka yi wa kaciyar.

Wannan dai wata al'ada ce da kasashen da ke yankin kahon Afirka da yankin yammacin Afirka da Kudancin Afirkan da kuma kasashen yankin Asiya. wani kiyasi da kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkin mata suka bayar na nuni da cewa kasar Somaliya ce kan gaba awajen wannan dabi'a ta yi wa yara mata kaciya, inda kiyasin ke cewa akalla kaso 98 cikin dari na mata da shekarunsu ya kama daga 15 zuwa 49 an musu kaciya. Haka ma abin yake a makwabtan kasar na Habasha wato Ethiopia da kuma Sudan, inda a nan ma sama da kaso 70 na matan kasar suka fuskanci wannan mummunar al'ada ta yin kaciya.

Äthiopien Kampagne gegen weibliche Genitalverstümmelung

Yaki da yiwa mata kaciya a Ethiopia

Sophie Forrez ta kungiyar kare hakkin dan Adam da ke kasar Beljiyam mai suna Intact ta shaidawa tashar DW cewa a karkashin yarjejeniyarsamun mafaka a Turai ta Geneva ta 2015 an amince a bai wa duk wani wanda ke fuskantar tirsasawa ko kuma barazana a kasarsa mafaka, inda ta ce bisa wannan sharadi matan da ake wa kaciya a kasashensu na da damar neman mafaka a kasashen na Turai ta na mai cewa:

"Matan da suke fargabar fuskantar kaciya za su iya samun mafaka sakamakon kasancewarsu a a karkashin wata al'umma ko kuma kabila da ke fuskantar barazana. Fargabar yi musu kaciya da suke da ita, na zaman fuskantar tursasawa."

Sai dai a tattaunawarta da DW Linda Ederberg daga kungiyar Terre des Femmes da ke Jamus, akwai banbanci wajen samun mafakar cikin kasashen kungiyar ta EU.

"Koda yake aakwai dalilai na jinsi da ke sanya wa a bai wa mutum mafaka, koda al'adar yi wa mata kaciya na yin barazana, da dama daga cikin matan da ake yin kaciya a kasashensu basu da masaniya, a kai, kana a wasu kasashen ba a bayyanasu kamar yadda yake a kasar Beljiyam ba. Sabo da haka ana iya yin watsi da bukatarsu ta neman mafaka. Ana ganin cewa al'adar yi wa mata kaciya na nan kuma ba ta kai dalilin bayar da mafaka ba. Amma idan su matan za su iya yin bayani yadda ya kamata na cewa ta na yi musu barazana, to za su iya samun mafakar."

Weibliche Genitalverstümmelung Somalia

Taron fadakarwa kan al'adar kaciya wa mata a somaliya

Sai dai a nan Turai ma matan da dama basu tsira daga wannan al'ada ta yi musu kaciya ba. Wani kiyasi ya nunar da cewa mata kanana da manya 180.000 ne suka fuskanci kaciyar a nan nahiyar Turai, ko da yake babu cikakken lissafi kan adadinsu. Walter Lutschinger shine manajan darakta na cibiyar Desert Flower da ke kasar Ostiriya, duk da dokar da ake da ita a Turai baki daya wadda ta haramta yi wa matan kaciya, hakan bai kare matan da kaciyar ke zaman al'adarsu ba.

"A nan ma ana yi wa matan kaciya tamkar a Afirka ko wasu sassan Asiya. Yaran ba su da wata kariya. Koda yake akwai dokoki a Turai baki daya, sai dai ba a sanya idanu a kansu."

Wani binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya gudanar na nuni da cewa akalla mata miliyan 150 ne a duniya suka fuskanci matsalar kaciyar inda a duk shekara ake samun matmiliyan uku da ake wa kaciyar a duniya.))

Sauti da bidiyo akan labarin