1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Kastina: Tura ta kai bango kan tsaro

September 13, 2022

Al'ummar karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina sun fatattaki 'yan bindiga da suka kai musu hari, inda suka kashe da dama a cikinsu.

https://p.dw.com/p/4Gmtu
Najeriya | Katsina | Tsaro
Dama dai matasa a jihar Katsina da ke Najeriya, sun jima suna zanga-zanga kan tsaroHoto: DW/H. Y. Jibiya

Yankin karamar hukumar ta Batsari dai, na daga cikin yankunan da maharan ke gallazawa al'umma dare da rana. 'Yan bindigar dai sun shiga garin kan babura da makamai da niyyar suyi ta'addancin da suka Saba sai dai al'ummar garin sun ce tura ta kai bango, inda suka yi kukan kura tare da tinkarar maharan. Gwamnatin jihar Katsinan dai ta ce, abin da al'ummar Batsarin suka yi sun kyauta kuma akwai bukatar sauran al'umma ma su yi koyi saboda dama tuni ta ce kowa ya kare kansa.

A nasu bangaren masana tsaro kamar Dakta Kabir Adamu na nunar da cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya aminta da abin da al'ummar ta Batsari suka yi sai dai akwai bukatar su yi taka tsan-tsan saboda gudun bacin rana. Rahotanni dai sun nunar da cewa yanzu al'ummar jihohin Katsina da Zamfara da dama, sun tanadi makamai kuma suna kare garuruwansu dare da rana tin bayan da gwamnaticin jahohin suka bayar da damar kare kai. Hakan ne ya sa suka dau damarar tinkarar maharan ba gudu ba ja da baya.