Yada tsohon bidiyo ya tayar da rikici a Abidjan
May 21, 2021Binciken da aka gudanar bayan aukuwar lamarin, ya nuna cewa, wani tsohon bidiyo da ya karadde shafukan sada zumunta na zamani a ranar Larabar da ta gabata, da a ciki ya nuna yadda wasu da aka ce jami'an tsaron Nijar ne, na gallazawa wa wasu matasa 'yan Cote d'Ivoire, ya zama dalilin fadan da ya raunata wasu sama da dari baya ga asarar tarin dukiya.
Ana ganin an nadi bidiyon a Nijar tun a shekarar 2019. Ba a dai kai ga tantance sahihancin bidiyon ba. Gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta yi Allah-wadai da lamarin da ya kawo wannan rudanin, inda ta nemi a zauna lafiya. Tuni aka kaddamar da bincike bayan kama wasu kimanin ashirin da ake wa tambayoyi. Kasar da ta kasance a sahun gaba a noman Koko a duniya, ta bar kofofinta a bude ga masu son aiki a gonakin kokon, jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen yankin da 'yan kasar ke shiga don neman abin yi.