Najeriya-gwamnati na son tsawaita dokar ta-baci
November 20, 2014Talla
A dai-dai lokacin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace garuruwa da dama a jihohin nan uku da ke fama da tashin hankali sakamakon kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar duk da dokar ta bacin da jihohin suka kwashe sama da tsahon shekara guda a karkashinta, gwamnatin ta dauki aniyar sabunta dokar ta bacin a jihohin na Adamawa da Borno da Yobe.