Zanga-zangar adawa da dokar ta-baci | Siyasa | DW | 19.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar adawa da dokar ta-baci

Matasa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun kashedi ga duk wani sanata ko dan majalisar wakilai da ya amince da kara wa’adin dokar ta baci a jihohinsu

Haka kuma matasan sun bayyana cewa za su yi bore irin wanda aka yi a kasashen Larabawa, domin nuna adawar su matukar aka amince da kara wa'adin dokar a karo na hudu.

Matasan shiyyar Arewa maso bagashin Najeriya musamman wadanda suka fito daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda sune suka fi dandanar azabar dokar ta-baci da ta shafe shekara daya da rabi, ba tare da ganin tasirin ta ba. Don haka sun ce ba zasu taba lamuntar sake sabunta wannan wa'adin doka karo na hudu ba.

Matasan wanda yawanci ke cikin fushi da kokarin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, na kara tsawaita dokar ta-baci a jihohin da rikicin Boko Haram ya yi kamari, sun ce za su turjewa duk wani kokari na samun nasarar tsawaita wannan doka a jihohin su. Saboda haka ne suka aike da sakon gargadi ga ‘yan majalisun dattawa da na wakilai da su guje wa yin abinda zai iya kara musu kuncin rayuwa ta hanyar tsawaita wa'adin dokar.

Wadanan matasa wanda ke samun goyon bayan shugabannin su, sun kuma shirya yin gangami domin bore wa shugabannin da ‘yan majalisun yankin jihohin uku, matukar dai suka amincewa bukatar shugaban na tsawaita dokar.

Sai dai jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Borno ta ce ita kam magoya bayanta sun amince a tsawaita wannan wa'adin dokar ta-baci, da suke ce ta haka ne kawai za'a iya magance matsalar tsaron da ke addabar yankin.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin jihohin Borno ta bayyana matsayin ta dangane da wannan dokar ta bacin. Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ce babban abin da ake bukata shi ne jami'an tsaro su yi ayyukan su, kuma kar su yi abinda zai haifar da matsala ga zabubbukan da ke tafe.

Masharhanta dai na ganin ya zama wajibi a tsaya, a duba wannan bukatu na matasa da sauran jama'ar jihohin, kafin yanke hukunci kan tsawaita wannan doka.


Sauti da bidiyo akan labarin