Tsaka mai wuya kan yarjejeniyar CETA | Labarai | DW | 23.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaka mai wuya kan yarjejeniyar CETA

A ranar Litinin din nan ce kungiyar tarayyar Turai EU da kuma kasar Kanada za su yanke hukunci a kan makomar yarjejeniyar cinikayya ta CETA da za su kula

Kungiyar tarayyar Turai ta bai wa kasar Belgium wa'adi zuwa gobe Litinin ta shawo kan yankunanta da ke adawa da yarjejeniyar cinikayya ta CETA tsakanin Kungiyar ta EU da Kanada. Kungiyar ta ce idan Beljiyam din ba ta cimma matsaya ba to kuwa yarjejeniyar da za'a kulla wadda ake fatan za ta bunkasa tattalin arzikin bangarorin biyu za ta rushe. A halin da ake ciki dai mashawarta kan harkokin cinikayyar sun nufi kasar ta Beljiyam domin taimaka wa wajen sassauta damuwa a kan gwamnatin kafin cikar wa'adin. A bangarenta Kanada ta ce a shirye ta ke ta sanya hannu a kan yarjejeniyar kamar yadda aka tsara wanda kuma aka shafe shekara guda ana tattauanawa da ministar ciniki ta kasar Crystia Freeland.