Tsageru za su koma ta′adi a Najeriya | Labarai | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsageru za su koma ta'adi a Najeriya

'Yan bindigar yankin Naija Delta mai arzikin mai a Najeriya sun ce tsagaita buda wuta da suka yi kan bututan mai, ya zo karshe.

Mayakan tarzoma a yankin Naija Delta mai arzikin mai a Najeriya sun ce tsagaita buda wuta da suka yi kan bututan mai, ya zo karshe. Wata sanarwar da suka wallafa a shafin Intanet a wannan Juma'ar, kungiyar ta Niger Delta Avengers, ta ce rijiyoyin mai da ke yankin za su fara fuskantar hare-hare.

Kasar ta Najeriya dai ta ji a jikinta ashekarar da ta gabata, sakamakon hare-haren da mayakan kungiyar suka sha kaddamarwa kan cibiyoyin mai da ke yanki kudancin kasar. Hare-haren nasu dai sun kaiga rage man da kasar ke hakowa matuka, wanda ba a sake ganin irinsa ba kimanin shekaru 30 da suka gabata.