Tsagaita wuta tana tangal-tangal a kasar Siriya | Labarai | DW | 27.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagaita wuta tana tangal-tangal a kasar Siriya

Tsagaita wuta a rikicin Siriya ya gamu da cikas sakamakon hare-hare da aka samu da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.

Wani yaro karami yana cikin mutanen bakwai da suka hallaka a yankin gabashin Ghouta na kasar Siriya, jim kadan bayan ayyana tsagaita wuta da ke samun goyon bayan Rasha, kamar yadda masu raji kare hakkin dan Adam suka tabbatar. A daya bangaren mahukunta na Rasha sun ce kwashe fararen hula daga cikin yankin na Siriya da aka amince da tsagaita wuta ya danganta da 'yan tawaye masu dauke da makamai na cikin yankin.

Akwai kimanin fararen hula 400,000 a yankin da ke kusa da birnin Damascus fadar gwamnatin kasar ta Siriya. Tun farko Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan shirin na tsagaita wuta. Ita dai kasar Rasha ta kasance wata kasa mai girma wadda ta goyi bayan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ta Siriya a daukacin yakin basasan na Siriya.