Toshe Intanet a Kamaru da gudun hijira a Sudan ta Kudu sun dauki hankalin Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Toshe Intanet a Kamaru da gudun hijira a Sudan ta Kudu sun dauki hankalin Jaridun Jamus

Jaridun Jamus sun yi nazarin matsalolin da ke tattare da toshe hanyoyin Intanet a arewacin Kamaru da na 'yan hijira daga Sudan ta Kudu da ke ketarawa zuwa cikin kasar Yuganda.

To za mu fara sharhin jaridun na Jamus a kan nahiyar Afirka ne da jaridar Die Tageszeitung.

A sharhinta mai taken watanni uku bayan toshe kafofin Intanet a yankin Kamaru da ke amfani da harshen Ingilishi, a karshe an sami sa'ida bayan da gwamnati ta bada umarnin mayar da harkokin sadarwar ta Intanet a ranar Alhamis.

Kasar ta Kamaru wadda ta taba zama karkashin mulkin mallakar Jamus ta kasance ikon Birtaniya da Faransa bayan yakin duniya na biyu, musababbin da kasar ta ke amfani da harsunan Faransanci da Ingilishi na Iyayen gijinta.

Kashi 20 cikin 100 ne na al'umar kasar suka fada yankin da ke amfani da turancin Ingilishi wadanda kuma suka kasance marasa rinjaye.

Maida yankin saniyar ware da gwamnatin ta yi inji jaridar ya sanya a bara lauyoyi a Bermanenda daya daga cikin manyan biranen kasar suka gudanar da zanga zangar neman bullo da tsarin tarayya na federaliyya tare da sakarwa bangaren Ingilishin mara.

Matakin gwamnati na amfani da karfin sojoji wajen tarwatsa zanga-zangar da ta kai ga hasarar rayukan wasu dalibai ya haifar da karin tunzuri da rufe marakarantu a yankin.

Jaridar ta nuni da cewa katse harkokin na Internet ya yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar alal misali ta ce kamfanoni sadarwa sun yi hasarar kimanin Dala miliyan hudu da rabi a tsawon kwanaki 90 da aka toshe kafofin na Internet.

A karshe jaridar ta die tageszeitung ta ce fafatukukar kungiyoyin farar hula da suka samar da maudu'in BringBackOurInternet ya yi tasiri sai dai kuma ya kamata gwamnati ta banbance aya da tsakuwa a yakin da take yi da ta'addanci domin kaucewa take hakkin jama'ar da basu ji ba basu gani ba, kamar yadda kungiyoyin farar hula a kasar suka nunar.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung a nata sharhin ta tabo batun 'yan gudun hijira ne a Sudan ta Kudu da ke ketara kan iyaka zuwa cikin Yuganda mai makwabtaka.

Jaridar ta ce a kowace rana mutane kimanin dubu uku ne ke yin hijira daga Sudan ta Kudu suna ficewa domin tsira da rayukansu a sakamakon yakin basasa da kuma annobar yunwa uwa uba da kuma gwamnatin da ta yi shakulatin bangaro da makomarsu.

Jaridar ta ce ya zuwa barazanar bara lokacin da yakin basasar na shekaru uku ya yi tsanani yan gudun hijira dubu 620 ne suka tsallaka zuwa cikin Yuganda, yayin da a bana kadai mutane dubu 175 suka ketara iyakar Yuganda bisa alkaluman hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta baiyana cewa wannan shi ne tagaiyara mafi girma na 'yan gudun hijira a Afirka.

Jaridar ta kara da cewa kasar Yuganda wadda ke da yawan al'umma miliyan 40, kwararar 'yan gudun hijira na zame mata babban kalubale. Sai dai ta ce sabanin wasu kasashen Afirka inda a kan nuna kyama ga yan gudun hijirar, kamar yadda 'yan cirani suka fuskanta a Afirka ta Kudu, Yuganda ta karbi 'yan gudun hijirar hannu biyu biyu. Jaridar ta ce wannan ya kasance babban abin misali kuma abin koyi ga wasu.

A yanzu haka hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na aiki tare da Yuganda domin taimakawa 'yan gudun hijirar da aka tsugunar sansanin Bidi Bidi da ke arewa maso yammacin kasar.

Batun makamashin hasken rana a Kenya shi ne ya dauki hankalin Jaridar Süddeutsche Zeitung

Jaridar ta yi tsokaci a kan sabuwar dokar da gwamnati ta bullo da ita wadda ta bukaci masu gidaje su kafa makamashin Sola a gidajensu ko kuma su fuskanci zuwa gidan jarun.

Dokar ta wajabta wa masu gidajen otel da makarantu da gine-gine na harkokin kasuwanci da ke da dakuna fiye da uku da kuma ke amfani da ruwa fiye da lita 100 a rana da cewa tilas ne su kafa sola.

Gwamnatin ta sanya hukunci tarar euro dubu goma ko kuma dauri a gidan yari ga duk wanda ya saba dokar. Gwamnatin Kenyar ta dade tana kokarin rage yawan amfani da wutar lantarki inda take fadakarwa ga amfani da makamashin hasken rana na Sola.