1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya musanta labarin rashin lafiyarsa

March 23, 2023

Zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya musanta labarin da ake yadawa game da koshin lafiyarsa. Dan siyasar dai ya fice daga Najeriya a jiya Talata zuwa London.

https://p.dw.com/p/4P6Rl
Bola Tinubu
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa ba ya da koshin lafiya, inda kwamitin yakin neman zabensa ke cewa ya ziyarci wajen Najeriyar ne domin ya huta tsananin gajiyar yakin neman zabe ta yadda zai kintsa wa karbar mulki.

'Yan Najeriyar da dama dai na maida hankali kan lafiyar Bola Tinubu a kasar da a baya aka samu shugaban da ya rasu bayan fama da rashin lafiya mai tsawo.

Shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari ma dai na yawan tafiye-tafiyen ganin likita a ketare, inda a farkon shekarar 2017 ma ya yi zaman watanni uku a Burtaniya a kan cutar da ba a bayyana ba.

Zababben shugaban na Najeriya dai ya yi ta fitowa a wasu hotunan bidiyo babu karsashi lokacin yakin neman zabensa inda kalamansa da ma yanayin kuzarinsa ke nuna yadda karfi ke kare masa.

A halin yanzu ma dai manyan 'yan takarar shugabancin kasar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour, na kalubalantar nasarar Bola Tinubu a kotu.