1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin CAN sun gana da Bola Tinubu

November 16, 2022

Dan takarar shugaban kasa na APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN kan zabin abokin takararsa a zaben kasar na shekarar badi.

https://p.dw.com/p/4JcmC
Nigeria l APC Ergebnis l Präsidentschaftskandidat
Shugaba Buhari da Bola TinubuHoto: Nigeria Prasidential Villa

A baya dai can din ba ta boye adawarta da kokarin samar da takarar musulmi da musulmi a cikin jam'iyyar APC mai mulki. Har ma ta kai ga shugabannin addinin kirista nesa kansu da takarar da suke fadin ba ta da ra'ayin kiristocin cikin kasar.

A ranar Laraba (16.11.2022) ne dai aka yi zube ban kwarya a tsakanin bangarorin guda biyu a karon farko tun bayan fara takara ta Tinubun.

Kungiyar CAN din dai ce ta gaiyyaci Tinubun ta kuma karanta masa wasu jeri na bukatu dai dai har 11 da ta ce tana da bukatar jin amsarsa kafin iya kai wa ga yanke hukunci bisa kansa a zaben na shekarar badi.

Dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu
Dan takarar APC Bola Ahmed TinubuHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

To sai dai kuma hada fuskar ta koma dama ga  Jagaban na kai yakin nasa ya zuwa gida na shugabanni na kiristocin tarrayar Najeriyra da ya ce sun wuce makadi cikin rawa wajen matsayin na su.

"Zabina na Shetima, wannan ya kawo ne ga tambayar  da ke zuciyata da dama. Me ya sa na zabi Sanata Shettima, me yasa na zabi tikitin addini guda daya? Wadannan ba su da wani tasiri ga kokarin inganta kasarmu. Ban zabi Sanata ba domin mu zama masu addini guda daya, na zabe shi ne Saboda ina son mu kafa gwamnatin da za ta samar da ci gaban da kasarmu ke da bukata. Bari in bude muku zuciyata. Na zabi Shetima ne saboda ina neman mutumin da zai taimaka mun da mulki, maimakon wanda zai taimaka mun a ibada."

Wannan ne dai karo na farkon fari da Tinubun ke fuskantar masu adawa da batun zabin nasa wajen baiyana hujjojjin zaben na sa.

To sai dai kuma ita kanta amincewa da ganawa da Tinubun da tun da farkon fari shugabanni na kungiyar suka nuna fushinsu a kansa dai, a fadar Dr Abdullahi Umar Ganduje da ke zaman gwamnan jihar Kano, kuma daya a cikin 'yan tawagar Tinubun na nuna alamun sauyin taku a bangare na malaman addinin.

Wakilan mabanbantan addinai a Najeriya
Wakilan mabanbantan addinai a NajeriyaHoto: DW/U. Abubakar Idris

Bakin ciki da ikon Allah ko kuma kokari na neman adalci dai, duk da cewar dai Tinubun ya ce yana bukata ta lokaci kafin iya kai wa ga yanke hukunci bisa bukatun CAN din,  daga dukkan alamu Tinubun ya na da sauran tafiya a tsakaninsa na shawo kan malaman addinin na Kirista.

Watsi da shawara ta kwararru ko kuma neman mafita ta siyasa dai, ana kallon rawa ta malaman addinin da kokari na wuce gona da iri a cikin tarrayar Najeriyar da ke fuskantar rabuwa.

To sai dai kuma duk da tsananin da ke akwai bisa banbancin hanya, a fadar Reverend Gedion Para Malam da ke zaman dan kwamiti na siyasa na kungiyar CAN din dai, kiristocin cikin kasar suna iya zabar Musulmi in hali yayi.

Abun jira a gani ya take shirin kayawa a kokari na zare bukata ta zuciya cikin fage na siyasar tarrayar Najeriyar da ke dada zafi yanzu.