1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tinubu na kan gaba a jihohi 12

Abdullahi Tanko Bala
February 27, 2023

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Lagos Bola Ahmed Tinubu yana kan gaba da yawan kuri'iu a sakamakon jihohji 12 daga cikin 36 da INEC ta baiyana

https://p.dw.com/p/4O2qA
Bola Ahmed Tinubu dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar APC
Hoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

Alkaluman sakamakon zaben sun nuna Bola Tinubu na Jam'iyyar APC na kan gaba da kuri'iu miliyan uku da dubu dari bakwai yayin da babban mai kalubalantarsa na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya ke da kuri'iu miliyan biyu da rabi.

Peter Obi na matsayi na uku da kuri'iu miliyan daya da dubu dari uku. Sai dai kuma Peter Obi na Jam'iyyar Labour ya kada abokin hamaiyarsa na jam'iyya mai mulki a jihar Lagos.

Kawo yanzu dai kimanin kashi biyu cikin kashi uku na jihohin kasar ba a baiyana sakamakon su ba tukunna.

Duk dan takarar da zai zama shugaban kasar sai ya sami mafi rinjayen kuri'iu, ya kuma ya sami kashi daya cikin kashi hudu na akalla jihohi 24.