1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Tinubu ya bayyana takainsa a kan sace dalibai

Abdourahamane Hassane
March 8, 2024

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da sace dalibai maza da mata da aka yi a Jihohin Kaduna da Borno.

https://p.dw.com/p/4dJVd
Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

A cikin  wata sanarwar fadar gwamnatin kasar   Tinibu ya ce ya samu  bayanai daga Jami'an tsaro,kan satar guda biyu, wanda ya ce ya bayar da umurni da a gaggauta cetosu. Sannan ya janjanta wa iyalan wadanda abin ya shafa yana mai ba su tabbacin cewar nan ba da dadewa ba za su sake haduwa da 'yan uwansu. A cikin wannan mako ne dai aka sace wasu mata kusan dari biyu a Jihar Borno, yayin da aka sake kame wasu daliban sama da dari biyu a   Kaduna.