1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Matan da aka sace a jihar Borno sun zarta 100, in ji hukuma

Mouhamadou Awal Balarabe
March 7, 2024

Wasu majiyoyi sun nunar da cewar adadin mata da suka bace a yankin Arewa maso gabashin kasar sun tasamma 100, bayan garkuwa da 'yan bindiga suka yi da wasu 'yan gudun hijira mata a karkarar Ngala da ke jihar Borno.

https://p.dw.com/p/4dGIa
Mata na shiga tasku sakamakon matsalar tsaro a arewacin Najeriya
Mata na shiga tasku sakamakon matsalar tsaro a arewacin NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/K. Palitza

Jami'in yada labarai na karamar hukumar Ngala Ali Bukar ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mazauna kauyen sun tabbatar da bacewar mutane 113 a halin yanzu. Dama ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce an yi garkuwa da mata sama da 200 da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a lokacin da suka je neman itace.

Karin bayani: Kokarin magance tsaro a arewacin Najeriya

Satar mutane don neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar matsala a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso gabashin Najeriya. Shugabannin mayakan sa-kai na zargin kungiyar ISWAP da marar hannu a  satar mutane. Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hau karagar mulki ne a  2023 ya yi alkawarin magance tabarbarewar tsaro da kuma barkewar rikicin kabilanci a jihohin tsakiyar kasar.

Karin bayani: Najeriya: Ina kudaden fansa suke shiga?

A Jihar Borno dai, ayyukan ta'addanci sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba miliyan biyu da muhallansu a cikin shekaru 15 da suka gabata.