1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamistan Britaniya za ta ziyarci kasashen Afirka

Salissou Boukari
August 28, 2018

A wannan Talatar ce firamistar Britaniya Theresa May ke soma ziyararta ta farko a matsayin firaminista a wasu kasashen Afirka, inda za ta soma daga Afirka ta Kudu sannan ta ziyarci Tarayyar Najeriya da kuma Kenya.

https://p.dw.com/p/33s7c
Theresa May
Hoto: Getty Images/Dunham

Firaminista May za ta tattauna batutuwan da suka shafi harkokin tsaro da kuma na kasuwanci a daidai lokacin da ta ke cikin tsaka mai wuya dangane da batun ficewarta daga Tarayyar Turai. May za ta yi wannan ziyara ce tare da rakiyar ministoci da wakilan 'yan kasuwa 29 daga masana'antu dabam-dabam inda za su ziyarci wadannan manyan kasashe uku na Afirka kamar yadda ofishinta ya sanar.

Firaministar ta Britaniya za ta kuma sanar da wani tallafin kasarta wajen yaki da matsalar tsaro da yankin ya ke fuskanta kamar yadda fadarta ta sanar kafin wannan ziyara. Theresa May za ta yi wani jawabi kan harkokin tattalin arziki a birnin Cape na Afrika ta Kudu sannan ta gana da shugaban kasar Cyril Ramaphosa da kuma 'yan kasuwa da dama.