Theresa May ta ci alwashin kare matsayinta
November 16, 2018Talla
Firaministar Birtaniya Theresa May ta sami goyon bayan wasu jiga jigan ministoci biyu na gwamnatinta yayin da take fadi tashin kare matsayinta a dambarwar ficewar Birtaniyar daga kungiyar tarayyar Turai EU.
Wannan dai na zuwa ne bayan da a ranar alhamis wasu ministocin gwamnati su hudu suka ajiye mukamansu domin adawa da shirinta na ficewar kasar daga kungiyar EU.
An dai sa ido ne akan ministan muhalli Michael Gove wanda ya kada kuri'ar ficewa.
A waje guda kuma Firaminista Theresa May ta cike gurbin ministoci biyun da suka yi murabus.
Ta ci alwasin cigaba da kare daftarin yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar Tarayyar Turai, tana mai cewa yarjejeniya ce da za ta amfani jama'ar Birtaniya.