Theresa May na nadin ministoci | Siyasa | DW | 14.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Theresa May na nadin ministoci

Sabuwar Firaministar Birtaniya Theresa May ta fara nada ministocin da za su jagoranci majalisar zartaswa ciki har da Boris Johnson, yayin da kasar ke daukar matakan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai EU.

Saurari sauti 02:59

Rahoto kan nadin ministoci a Birtaniya

Babban kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin ta Birtaniya bayan saukar tsohon Firaminista David Cameron, da kuma danka ragamar gudanarwa ga Theresa May da ake wa lakabi da jajircacciyar mace dai, shi ne yadda za ta fara daukar matakan ficewa daga kungiyar ta Tarayyar Turai wato EU sakamakon yadda batun ke cike da rarrabuwar kawuna da sarkakiya.

A jawabin da ta yi Firaminista May ta ce:

"Biyo bayan kuri'ar raba gardama, za mu fuskanci gagarumin sauyi a kasarmu. Yayin da muka fice daga Tarayyar Turai EU, za mu samar wa kanmu mafita mai kyau a duniya."

Großbritannien Theresa May bei der Queen

Sarauniyar Ingila ta yi na'am da May a matsayin Firaminista

Firaminista May ta nada mata a wasu manyan mukamai biyu, inda ta nada Liz Truss a matsayin sakartariyar harkokin shari'a, bayan da ta kori tsohon ministan shari'ar Michael Gove, babban mai gangamin Birtaniya ta ci gaba da kasancewa cikin EU. Sannan an nada tsohuwar mai kula da harkokin bunkasa kasashe ta kasar Justine Greening, a matsayin sakatariyar ilimi kana ministar kula da harkokin mata da daidaito.

Boris Johnson ya zama ministan harkokin waje

Sabuwar Firaministar ta kori ma'aikata da dama da suka yi aiki tare da Cameron, kana ta yi sabbin nade-nade ciki kuwa har da na sakataren harkokin cikin gida kana mai kula da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai EU. Wani abu da ya bada mamaki shi ne nadin da ta yi wa Boris Johnson a matsayin sakataren harkokin kasashen ketare wanda hakan ke nuni da cewa Birtaniyar da gaske take kan batun ficewa daga Tarayyar Turai.

Großbritannien Kabinett Philip Hammond

Philip Hammond ya tashi daga ma'aikatar waje zuwa na kudi

Shi kuwa tsohon sakataren harkokin kasashen ketaren na Birtaniya Philip Hammond a yanzu Firaminista May ta nada shi a matsayin sakataren kudi: Sai dai ya ce akwai babban kalubale a gabansa. Hammond ya ce: "Kalubale na farko da zan tunkara shi ne daidaita tattalin arziki, da kuma samun tabbaci a nan gaba."

A yayin da yake bayyana ra'ayinsa kan sabuwar Firaministar ta Birtaniya Theresa May ministan harkokin cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere cewa ya yi: " Tana da jajircewa, kana tana sukan duk abin da bai yi mata ba da yin aiki yadda ya kamata, mutum ce da za a iya dogaro da ita a matsayin amintatta.."

Ana sa ran dai Firaminista Theresa May za ta kasance kan karagar mulki har zuwa shekara ta 2020.

Sauti da bidiyo akan labarin